”Yan bindiga sun kashe mutum 11 tare da raunata wasu a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kisan mutane shida a kauyen Badarawa dake yankin karamar hukumar Shinkafi a jihar. Kakakin ‘yan sandan jihar ta Zamfara, Mohammed Shehu ya fada wa majiyar BBC cewa, wasu mutum 10 kuma sun ji rauni a harin. Shehu ya ce, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji sun shiga […]

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Zamfara, Mohammed Shehu ya fada wa majiyar BBC cewa, wasu mutum 10 kuma sun ji rauni a harin.
Shehu ya ce, jami’an ‘yan sanda tare da sojoji sun shiga daji domin farautar maharan.
To sai dai bayanan da ke fitowa daga kauyen na Badarawa sun ce mutum 11 ne aka kashe yayin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan wani taron jama’a.
Bayanan sun ce galibin wadanda lamarin ya rutsa da su matasa ne.
Haka ma an ce wasu mutanen 23 sun samu raunuka lokacin da ‘yan bindigar suka kai wannan harin.
Tuni dai aka yi jana’izar mutane da suka riga mu gidan gaskiya a harin da aka kai.