’Yan bindiga sun kashe mutum 12 a harin gidan mujallar Faransa (1)

’Yan bindiga da aka ce su uku ne sun hallaka mutum 12 a harin da suka kai gidan mujallar zanen takala ta Charlie Hebdo da ke kasar Faransa a shekaranjiya Laraba.Hudu daga cikin fitattun masu zanen takalar ciki har da Editanta suna daga cikin wadanda aka kashe da kuma ’yan sanda biyu.Kamfanin Dillancin Labarai na […]

’Yan bindiga sun kashe mutum 12 a harin gidan mujallar Faransa (1)
’Yan bindiga sun kashe mutum 12 a harin gidan mujallar Faransa (1)

’Yan bindiga da aka ce su uku ne sun hallaka mutum 12 a harin da suka kai gidan mujallar zanen takala ta Charlie Hebdo da ke kasar Faransa a shekaranjiya Laraba.
Hudu daga cikin fitattun masu zanen takalar ciki har da Editanta suna daga cikin wadanda aka kashe da kuma ’yan sanda biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP da ya ruwaito rahoton ya ce tuni ’yan sanda suka fara binciken kwakwaf don gano mutanen uku da suka gudu a wata mota.
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce babu shakka a kan cewa wannan wani hari ne na ta’addanci “mai cike da rashin imani.”
An ce shi ne hari mafi muni a kasar Faranasa tun 1961, lokacin da masu tsaurin ra’ayi da suke son Faransa ta ci gaba da rike kasar Aljeriya suka sanya bam a cikin jirgin kasa inda mutum 28 suka hallaka.
Maharan wadanda suka rufe fuskokinsu sun bude wuta ne da manyan bindigogi a cikin ofishin mujallar kuma suka yi musayar wuta da ’yan sanda a kan hanya a waje kafin su tsere a mota. Daga baya sun jefar da motar a unguwar Rue de Meaud, da ke Arewacin birini Paris, inda suka kwace wata mota ta biyu.
Editar mujallar Charlie Hebdo, Stephane Charbonnier da ke amfani da sunan Charb mai shekara 47, ya samu sakonnin barazanar kisa, inda aka hada shi da ’yan sanda don tsaronsa.
Jaridun kasar Faransa sun bayyana sauran masu zanen da aka kashe a harin da Cabu da Tignous da Georges Wolinski da kuma mai ba mujallar gudunmawa kuma masanin tattalin arziki dan Faransa Bernard Maris. Harin ya zo ne a daidai lokacin taron kwamitin editoci na mujallar na kullum-kullum. Kuma an yi munanan raunuka ga wasu mutum biyar.
Mujallar ta rika jawo cece-kuce a baya wajen yin zanen takala ciki har da wadanda ta rika cin zarafin Manzon Allah (SAW), wanda hakan ya tunzura wasu Musulmi suka sanya wa ofshinta wuta a watan Nuwamban shekarar 2011.
Shugaba Barack Obama na Amurka da Firayi Ministan Ingila Dabid Cameron da Shugaban Rasha bladimir Putin sun la’anci harin tare da nuna goyon bayansu ga Faransa tare da alkawarin hada hannu don yaki da ta’addanci.