’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya
Wanda ya kai kuɗin fansa ya bayyana yadda ya sha wahala kafin sako mahaifinsa.

Dajin da Sheikh Gumi ya yi wa ‘yan bindiga da’awa a Jihar Neja, daya daga jihohin da ke fama da matsalar tsaro. (Tsohon hoto).
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta.
- An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya
- Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
Masu sana’ar Gwari da abin ya shafa ’yan kasuwar Ɗan Magaji ne daga Ƙaramar Hukumar Zariya, a Jihar Kaduna.
Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin waɗanda suka tsira, waɗanda suka ji raunuka, da kuma waɗanda aka sako bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu.
Muhammad Zaharraddeen Sharaihu shi ne mutumin da ya kai wa ’yan bindigar kuɗin fansa domin a sako mahaifinsa da wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a dajin Katsina.
Zaharraddeen, ya ce tun yana kan hanya ‘yan bindigar suka riƙa kiran wayarsa har sai da ya isa inda suka ce ya tsaya.
Daga nan suka umarce shi da ya hau babur, sannan suka ce ya tsaya a wani waje don miƙa musu kuɗin.
Bayan ya miƙa kuɗin, wani mutum ya karɓa daga hannunsa, sannan aka umarce shi da ya koma bakin hanya ya jira fitowar ’yan uwansa.
A cewarsa, tun ƙarfe 1 na rana sai kusan Magariba aka sako mahaifinsa da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
Mutum huɗu da aka biya miliyan biyu kafin a sako su sun haɗa da Malam Sharihu Umar Shehi, Malam Magaji Idris, Lawal Gambo Kwalano da Ida Ɗan Gwari
Lamarin ya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin, inda jama’a ke fargabar ci gaba da ayyukan kasuwancinsu a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.