’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Sakkwato

Maharan sun sake yunƙurin kai hari yayin da ake gudanar da jana’izar waɗanda aka kashe, amma jami’an tsaro sun fatattake su.

’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a Sakkwato

Aƙalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan da ’yan bindiga suka kai hare-hare a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Harin, wanda ya faru tsakanin daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a, ya yi sanadin mutuwar mutum shida a ƙauyen Mazau, huɗu a Turtsawa, mata biyu, sannan da safiyar Juma’a maharan suka kashe wasu manoma uku a ƙauyen Tsamaye yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun fara yunƙurin kai hari ƙauyen Lalle, amma haɗin gwiwar sojoji da ’yan sa-kai da suka tunkare su ya tilasta musu ja da baya bayan shafe sa’o’i ana musayar wuta.

Wani mazaunin yankin, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun yi asara a fafatawar, sai dai sun kwashe gawarwakinsu kamar yadda suka saba.

Ya ce bayan sun gaza shiga Lalle ne suka nufi Mazau da Turtsawa inda suka kashe mutane, sannan suka dawo da safiyar Juma’a suka kashe manoma uku a Tsamaye.

Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun sake yunƙurin kai hari yayin da ake gudanar da jana’izar waɗanda aka kashe, amma jami’an tsaro sun fatattake su.

Wani jagora a Sabon Birni ya tabbatar da faruwar hare-haren, yana mai cewa ’yan bindiga na ci gaba da matsa lamba a yankin. Ya ƙara da cewa a ranar Laraba ma sun yi garkuwa da manoma uku a yankin.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har zuwa lokacin bai samu rahoton lamarin ba.