‘Yan bindiga sun kashe mutum 16 a sabon hari a Filato

Gwamnan jihar ya bayyana bacin ransa, kan harin da aka kai.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 16 a sabon hari a Filato

Akalla mutum 16 ne suka rasa rayukansu a kauyen Mushu da ke Karamar Hukumar Bokkos a Jihar Filato.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Kyaftin Oya James ne, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

A cewar Kyaftin James, an kai harin ne a daren ranar Asabar yayin da mazauna yankin ke tsaka da barci.

Ya kara da cewa, “bayan harin, an tura jami’an tsaro domin dakile rashin doka da oda a yankin. Amma an shawo kan lamarin.”

A halin da ake ciki, Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ya ce gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta kamo wadanda suka kai harin tare da tabbatar da sun fuskanci doka.

Bare, ya ce gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin, inda ya bukaci al’umma a fadin jihar da su sanya ido sosai, tare da kai rahoton duk wani abun zargi ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.

Ya ce: “muhimmancin hadin gwiwa tsakanin al’ummomin karkara, abu ne mai matukar amfani kuma akwai bukatar mutane suke bai wa jami’an tsaro hadin kai don fatattakar ‘yan ta’adda.”