Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Kudancin Kaduna

Dagacin kauyan Aboro, Shu’aibu Galadima ya bayyana cewa akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hari da wasu ’yan bindiga suka kai kauyan Angwar Dauda da ke karamar Hukumar Sanga, a Jihar Kaduna.A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu mutane suka kai hari a kauyan da misalin karfe biyu na dare. Dagacin […]

Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Kudancin Kaduna
Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Kudancin Kaduna

Dagacin kauyan Aboro, Shu’aibu Galadima ya bayyana cewa akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hari da wasu ’yan bindiga suka kai kauyan Angwar Dauda da ke karamar Hukumar Sanga, a Jihar Kaduna.
A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu mutane suka kai hari a kauyan da misalin karfe biyu na dare. Dagacin ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga jami’an NEMA, lokacin da suka kai masu tallafin kayan masarufi a yankin.
A cewarsa, akasarin mutanen kauyan na Aboro da suke zaune cikin sansanin ’yan gudun hijira a sakamakon rikicin baya, sun watse a saboda karar tashin bindiga da suka rika ji cikin dare. Sun kuma gudu ne saboda tsira da rayukansu.
“Sun kawo harin da misalin karfe biyu na dare ne a ranar Lahadi a Angwar Dauda. Jama’a kuma duk sun gudu daga sansaninsu da aka ajiye su domin tsira da rayukansu.” Inji shi.
Basaraken ya kuma ci gaba da cewa taimakon da hukumar ta NEMA ta kai wa jama’ar da abin ya shafa zai taimaka matuka wajen saukake musu radadin da suke ji, musamman na hasarar dukiyoyin da suka yi.
 Ya kuma roki sauran masu hali da kungiyoyi da gwamati da su kai wa mutanen yankin taimako, sannan ya yi addu’ar Allah Ya maido masu da zaman lafiya a yankin.
Tun farko, Hajiya Amina Ahman, wacce ta jagoranci tawagar NEMA zuwa wannan kauye domin raba masu wannan tallafi, ta ce hakkin hukumar ce ta taimaka wa wadanda abin ya shafa. Ta kuma roki jama’ar yankin da su daure su rika zamsn lafiya da junansu.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista