’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Kaduna

Maharan sun rika harbi a duk wani wuri da suka ga motsin mutune.

’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Kaduna

‘Yan bindiga

Akalla mutum 18 ciki har da wani jami’in dan sanda sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da ’yan bindiga suka kaddamar kan wasu yankuna biyar a Jihar Kaduna.

Yankunan da abin ya shafa da ke cikin Masarautar Chawai a Karamar Hukumar Kauru sun hada da Kigom, Kikoba, Kishisho da Unguwar Magaji.

Da yake zanta wa da Aminiya, wani mazaunin daya daga cikin yankunan da lamarin ya shafa, ya ce maharan da suka mamaye yankunan sun rika harbi a duk wani wuri da suka ga motsin mutane.

Bayanai sun ce an kashe mutum shida a Unguwar Magaji da wasu shidan a Kikoba sai mutum daya a Kigam da wasu biyar a Kishisho.

“Maharan sun salwantar da dukiya ta miliyoyin naira ciki har da gonaki a yankunan da suka kai harin,” a cewar mazaunin da ya bukaci a sakaya sunansa.

Sai dai neman jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ballantana bayar da amsar sakon kar-ta-kwana da ya aike masa.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki