’Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Zariya

An kai harin ne kwana daya bayan ginin masallaci ya kashe mutum 10

’Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Zariya

‘Yan bindiga

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari unguwar Kofar Gayan da ke Zariya a Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum 2 sannan suka yi awon gaba da wani mutumin.

Harin na zuwa ne kwana daya da rasuwar kimanin mutum 10 sakamakon ruftawar wani bangare na ginin babban masallacin Juma’a na Zariya da ke Kofar Fadar Sarkin Zazzau.

Majiyar jami’an tsaro ta sanar da Aminiya cewa maharan sun afka anguwar ne da misalin karfe 11:00 na dare inda suka rika harbe harbe kafin daga bisani suka bindige mutane biyu, kuma sukayi awon gaba da yaro daya.

Anguwar Kofar Gayan dai ta dade tana fama da hare-haren ’yan bindiga a yan shekarun baya a inda ake yawan kashewa tare da dauke mutane a kai a kai.

Ita ce kuma anguwar da aka dauke wani jami’in hukumar Kwastam wanda ya shafe kwanaki 69 a hannun mahara kafin daga bisani a sako shi bayan biyan kudin fansa.

Maharan wanda aka yi ittifakin ta wannan anguwa suke biyo sa’ilin kai mafiya yawan hare-haren suke kai wa a anguwan birnin Zariya, ko a ’yan kwanakin nan sun sake dauke wata wata matar jamin Kwastam da yarinyarta mai shekaru 3 inda suka sako ta a makon da ya gabata bayan shafe kwanaki sama 60.

Majiyarmu ta rawaito cewa mutanen da aka kashe sun hada Shamsuddeen na gidan Larabawa da kuma Shafi’u na gidan Malam Yusuf, dukkansu mazauna anguwar Kofar Gayan.

Majiyar ta kara da cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wani yaro daya mai suna Hamza Auwal, kafin daga bisani jami’an tsaro suka sami nasarar kubutar da shi.

Unguwar ta Kofar Gayan dai a nan babban asibitin Gambo Sawaba da gidaje masu saukin kudi wato ‘Lowcost’ suke.

Sai dai duk kokarin tuntubar Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalinge ya ci tura, sakamakon rashin samun wayarsa ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025