’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa

Rahotanni sun nuna cewar maharan sun hallaka mutanen biyu sakamakon jinkirin biya musu kuɗin fansa.

’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa.

Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa Rubochi.

Wani ɗan uwan mamatan, Shuaibu Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun nemi iyalan waɗanda lamarin ya shafa su biya wa kowa Naira 500,000 amma Naira 500,000 suka iya tattaraws baki ɗayansu.

“Shugaban maharan ya kira mu ranar Juma’a, muka sanar da shi cewa Naira 500,000 kacal muka samu. Ba mu san cewa tuni sun kashe su ba saboda jinkirin biyan kuɗin fansar ba,” in ji shi.

 

Abdullahi ya ce bayan haka, ’yan bindigar sun saki makiyayin da matar da suka sace bayan an biya su Naira miliyan uku a maɓoyarsu da ke cikin dajin Kotonkarfe, a Jihar Kogi.

Shugaban yankin Gwargwada, Ugbada Alhaji Hussaini Agabi Mam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace matasan ne a hanyarsu ta dawowa daga Rubochi.

“Abin takaici, an kashe matasan nan biyu saboda kawai danginsu sun yi jinkiri wajen biyan kuɗin fansa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ba a samu gawarwakin mamatan ba domin an kai su cikin dajin Kotonkarfe.

“Na samu labarin cewa shugaban Ƙaramar Hukumar Kotonkarfe ya tura maharba da jami’an tsaro don su shiga dajin su nemo gawarwakin, amma har yanzu ba su same su ba,” in ji shi.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.