’Yan bindiga sun kashe mutum 2 ranar Kirsimeti a Adamawa

Shugaban yankin ya ce suna zargin mayakan Boko Haram ne suka kai harin.

’Yan bindiga sun kashe mutum 2 ranar Kirsimeti a Adamawa

‘Yan sanda

’Yan sanda a Adamawa sun tabbatar da mutuwar mutum biyu ranar Kirsimeti a harin da aka kai yankin Kwapre da ke Karamar Hukumar Hong ta jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya shaida wa manema labarai a Yola ranar Talata cewa rundunar ta fara bincike kan lamarin.

A cewarsa, kwamishinan ’yan sandan jihar, Babatola Afolabi, ya tura ’yan sanda yankin domin gudanar da bincike.

Shi ma da yake tabbatar da labarin kisan, shugaban Gundumar Dugwaba, Mista Simon Buba, ya ce suna zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin na ranar Kirsimeti.

Rahotanni sun ce maharan sun mamaye yankin ne a kan babura, inda suka kwashe kayan abinci sannan suka tsere zuwa Dajin Sambisa.

Kakakin ’yan sandan ya bukaci jama’ar jihar da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk wani wani ko abu da ba su yarda da shi ba.

An harbe ’yan sanda biyu a Yobe

Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’