’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma a Neja
Al’ummar yankin sun koka don neman dauki daga gwamnatin jihar.
’Yan Bindiga sun kai hari kauyen Bassa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, inda suka kashe mutum biyu tare da raunata wani mutum daya.
An ruwaito cewar maharan sun kuma yi awon gaba da manoma ba a tantance adadinsu ba a yayin harin.
- Tsadar Rayuwa: Kwastam ta fara rabon kayan abincin da ta kwato
- NAJERIYA A YAU: Tallafin Da ’Yan Najeriya Ke Bukata
Mazauna yankin sun ce harin na ranar Alhamis, shi ne na biyu cikin mako biyu, inda suka ce maharan sun sace mutane da yawa tare da dabobbi masu tarin yawa.
Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, “Wadannan mutane suna kashe mu kuma muna ta neman agaji, kamar abin da ya faru a Allawa, inda suka kone gidajenmu, kayan abinci, gwamna. Shin gwamnati a shirye ta ke don ceton mu daga wadannan ‘yan ta’adda?
“Mun bar al’amuranmu ga Allah a yanzu don neman mafita domin gwamnati ba a shirye ta ke ta kare mu ba.”
Sai dai sakataren yada labarai gwamnan Jihar, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kawo karshen kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.
“Gwamnati za ta ci gaba da yin kokari wajen tunkarar kalubalen tsaro. Gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai don ganin an shawo kan lamarin.”
Jihar Neja dai na ci gaba da fuskantar kazaman hare-haren ta’addancin ’yan bindiga ba dare ba rana.