’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace wasu 3 a Bauchi

Maharan sun shiga gida-gida suna neman wasu matasa guda biyu.

’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace wasu 3 a Bauchi

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace wasu uku a wani hari da suka kai ƙauyen Rafin Ciyawa da ke Ƙaramar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya ce maharan sun kai hari ƙauyen, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutum uku.

“Eh, lamarin ya faru. ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Rafin Ciyawa, sun kashe mutane biyu sannan suka yi garkuwa da mutum uku.

“Mun tura jami’an ’yan sanda tare da mafarauta da ’yan banga zuwa yankin domin ceto waɗanda aka sace da kuma kama masu laifin,” in ji shi.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce maharan sun shiga garin da daddare, inda suka dinga harbe-harbe, lamarin da ya sa mutane suka tsere cikin daji domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin ƙauyen, Zubairu Yahaya, ya ce yaran da suka halarci karatun Alƙur’ani na dare suna barci a waje lokacin da harin ya faru.

“Da misalin ƙarfe 12:30 na dare muka ji ƙarar harbe-harbe. Da farko mun yi zaton ’yan banga ne ko ’yan sanda, amma daga baya muka gane ’yan bindiga ne.

“Bayan harbe-harben sun lafa, mun je wajen yaranmu, muka tarar da wasu sun ji raunuka, yayin da biyu suka mutu nan take,” in ji shi.

Ya ce lokacin da suke shirin kai waɗanda suka ji rauni asibiti, maharan sun sake dawowa.

“Sun riƙa bi gida-gida suna neman wani mai suna Saminu da ƙaninsa Safiyanu. Sun ce an ba su labarin cewa Saminu ya karɓi kuɗi masu yawa.

“Da suka ga ba su same shi ba, sai suka sace ’yan uwansa. Sai suk ce mutuwar yaranmu kuskure ne, domin ba su ne abin da suke nema ba.”

Zubairu, ya roƙi hukumomin tsaro su taimaka wajen ceto waɗanda aka sace tare da ƙara tsaro a yankin.

“Wannan shi ne karon farko da irin wannan hari ya faru a ƙauyenmu sama da shekara 50.”

Shi ma wani mazaunin ƙauyen, Malam Mukhtari Usman, ya ce maharan sun mamaye gidansa suna neman ƙaninsa.

Ya ce bayan sun kasa samun wanda suke nema, sun yi garkuwa da mata biyu, Rukkaya da Shamsiyya, da kuma wani namiji mai suna Kabiru.

A cewarsa, maharan sun kira shi a waya suna neman kuɗin fansa.

“Da farko sun nemi Naira miliyan 100, amma yanzu sun rage zuwa Naira miliyan 10. Har yanzu muna tattaunawa da su.”