’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato

Mazauna yankin sun nemi gwamnati ta ɗauki matakan kare al’umma.

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun kashe mutum uku a ƙauyen Torok da ke yankin Rim, Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Laraba, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Harin ya sa wasu mazauna yankin guduwa daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

An bayyana sunayen waɗanda aka kashe; Ezekiel Zakka, David Yakubu da Dauda Habila.

Ƙungiyar Matasan Berom (BYM) ta yi Allah-wadai da harin, inda ta bayyana shi a matsayin mummunan abu.

Ƙungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike tare da kamo waɗanda suka aikata laifin.

BYM, ta kuma buƙaci gwamnatin Jihar Filato da Gwamnatin Tarayya su ɗauki ƙarin matakai domin kare al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba.