’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara

Sun sace mutum takwas a yayin da suke tsaka da Sallar Magariba.

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.

’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa  da Birnin Yero.

A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu tara, ciki har da mata hudu.

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da fargaba.

A kauyen Birnin Yero, ’yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin sallar magariba, suka yi awon gaba da mutane takwas tare da raunata wasu da dama wadanda suka tsere zuwa cikin daji.

Sun kuma kai hari kauyen Shanawa, inda suka sace mutane hudu. Wannan harin ya faru ne kwana guda bayan an sako wasu mazauna kauyen guda 12 bayan an biya kudin fansa naira miliyan 12.

A Jangeru, an yi garkuwa da wata mata amma daga baya aka yi watsi da ita a cikin daji bayan da ’yan bindigar sun tabbatar ba za ta iya ci gaba da tafiya ba.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa sun sumar da ita ne, sai daga bisani ta dawo hayyacinta ta koma kauyensu.

’Yan ta’addan sun kuma gargadi mazuna kauyukan Kwari da Kurya, inda suka bai wa mazauna kauyukan wa’adin kwanaki uku su fice daga gidajensu ko kuma su fuskanci farmaki.

Sai dai mazauna kauyen Kurya sun sha alwashin yin fito-na-fito da wannan barazana, inda suka bayyana cewa sun gaji da biyan haraji da kudin fansa.

Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara yawan jami’an tsaro domin taimaka musu wajen kare kansu daga hare-hare a nan gaba.