‘Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace wasu da dama a Katsina

Maharan sun kai harin da rana tsaka, suka ci karensu ba babbaka.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace wasu da dama a Katsina

Jagoran ‘yan bindiga na Jihar Sakkwato, Bello Turji da tawagarsa.

Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun sake kai hari kauyen Dantsauni da ke Karamar Hukumar Batagarawa a Jihar Katsina, inda suka kashe mutum uku.

Daya daga cikin wadanda suka rasu, mai suna Abdulrashid Abba Manna, ya je gona da safe a kauyen Dantsauni amma ‘yan bindigar suka yi masa kwanton bauna suka kashe shi.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Babbar Ruga, Kwarin Maikotso da Kore, inda suka kashe mutum biyu tare da sace wasu takwas.

Kauyen Dantsauni dai na da nisan kilomita daya kacal daga kauyen Babbar Ruga.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma daruruwan mutane suka gudu zuwa cikin birnin Katsina domin tsira da rayukansu.

Wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma yi harbe-harbe a kan titin Katsina da ke kusa da garin.

Mazauna yankin sun ce ba a ga jami’an tsaro ba sama da minti 45 da ‘yan bindigar suka dauka suna tabargaza da rana tsaka.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce mutum daya ne ya mutu, wasu biyu kuma suka sami raunuka.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi