’Yan bindiga sun kashe mutum 30 a kauyen Filato

’Yan bindiga sun kashe mutum 30 a kauyen Tanknale da ke Karama Hukumar Mangu ta jihar Filato.

’Yan bindiga sun kashe mutum 30 a kauyen Filato

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun kashe mutum 30 da talatainin daren Talata a kauyen Tanknale da ke Karama Hukumar Mangu ta jihar Filato.

Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya ce  bayan samu rahoton cewa maharan suna harbi babu kakkautawa a kauyen ne, ‘yan sanda suka kai dauki aka fatattaki maharan wadanda har yanzu kai ga gano daga inda suka fito ba.

Sanarwar da Alabo ya fitar ta ce rundunar ‘yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaro na yin duk mai yiwuwa domin ganowa da kuma kamo masu hannu a harin don su fuskanci hukunci.

A yayin da ya ziyarci kauyen, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula da Binciken Manyan Laifuka na jihar, Bawa Sale, ya ce maharan sun tsere sun bar motarsu daya da babura guda hudu.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci jama’r yankin su kwantar da hankalinsu, jami’an tsaro na aiki domin cafke ‘yan bindigar.

Ya kuma yi kira gare su da su rika ba wa jami’an tsaro bayanai a kan lokaci domin daukar mataki da wuri.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan