’Yan bindiga sun kashe mutum 37 a kauyukan Sakkwato

Laifin mutanen shi ne kin biyan harajin da ‘yan bindiga suka saka musu

’Yan bindiga sun kashe mutum 37 a kauyukan Sakkwato

‘Yan bindiga

Rahotanni sun tabbatar da kisan akalla mutum 37 a wasu jerin hare-hare da ’yan bindiga suka kai kauyuka uku na Karamar Hukumar Tangazan Jigar Sakkwato.

Kauyukan da aka kai wa hare-haren sun hada da Raka da Raka Dutse da kuma Filin Gawa.

Shaidun gani da ido sun ce an farmaki kauyukan ne da yammacin ranar Asabar.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar wanda aka sauke a makon nan, Bashar Kalenjeni, lokacin da yake tabbatar da labarin ya ce an kashe mutum 18 a Raka, 17 a Filin Gawa, sai kuma 2 a Raka Dutse.

Ya ce, “Mun so mu je mu binne mamatan da daddare, amma maharan suka sake dawowa suka tarwatsa mu. Har zuwa safiyar nan ba a binne gawarwakin ba.

“Lifin ’yan kauyukan shi ne sun ki biyan harajin da maharan suka dora musu. Sun ce dole a fara biyan harajin nan take.

“Amma mutanen suka ki biya, hakan ne kuma ya sa suka kai musu hari, inda suka kashe 37 daga cikinsu. Wasu da dama daga cikinsu kuma sun ji rauni sakamakon harbin bindiga, kuma yanzu haka suna can suna karbar magani a Babban Asibitin Gwadabawa.

“Akwai kuma wadanda har yanzu ba a kai ga gano su ba. Yanzu haka muna jiran jami’an tsaro su zo su yi mana jagora don mu shiga dajin.,” in ji tsohon Ciyaman din.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya musanta labarin kai harin.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja