’Yan bindiga sun kashe mutum 49 a Zamfara
Gomman ’yan bindiga a kan babura sun sace fiye da mutum 100 a Zamfara.
Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 49 yayin da shafe kusan kwanaki biyar suna sheke ayarsu a Jihar Zamfara.
Aminiya kamar yadda mazauna suka ruwaito ta samu cewa an kashe mutanen ne a wasu kauyuk biyar naa Karamar Hukumar Anka a tsakanin ranar Talata zuwa Asabar.
Mazaunan sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun kashe mutum 18 a kauyen Farar-Kasa sai mutum 22 a Dangubi da wasu mutum biyu a kauyen Duhuwa sai hudu a Tsatsomawa da kuma wasu uku a kauyen ’Yar Sabaya.
Wani mazaunin garin Anka, Malam Idris Anka (ba sunan gaskiya ba) ya bayyana cewa tuna farkon makon da ya gabata ’yan bindigar suka rika kai hare-hare a kauyukan daban-daban.
Ya ce “a yanzu ta’addancin ’yan bindiga ya zama ruwan dare tamkar wata al’ada da ta zama rayuwar yau da kullum.
“Maganar gaskiya mun gaji da wannan barazana. ’Yan bindiga suna cin karensu babu babbaka tamkar babu wata gwamnati a kasar nan.
“Yanzu ’yan bindigar sun zame mana komai a cikin al’ummominmu — su na ’yan sanda, sarakunan gargajiya kuma shugabannin al’umma.
“Suna kai hari a duk lokacin da suka ga dama har da sanya mana haraji duk yadda suke so sannan babu wanda bai wuce su dauke shi ba kuma babu wanda ya isa ya ketare duk wani umarni da suka bayar.”
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da kyar ya tsere wa ‘yan bindigar a kan hanyar Anka zuwa Bagega a yau [Asabar] inda ya ce “’yan bindiga biyu sanye da kakin sojoji sun kafa wani shingen bincike a kan titin a yau [jiya] suna yi wa matafiya fashi da makami.”
Wani direben motar haya mai suna Mallam Bello Muhammad, ya roki gwamnatin tarayya da na jihohi da su kawo musu dauki ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro a yankin, domin a cewarsa rashin kasancewar jami’an tsaro na taimaka wa ’yan fashi a yankin.
Aminiya ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, wanda ya yi alkawarin tuntubar jami’in ‘yan sanda mai kula da sashen Anka domin jin cikakken bayani; sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kuma amsa kiran wakilinmu ba ballanta mayar da martanin sakon kar ta kwana da ya aike masa.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta yi watsi da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na shirin zaman lafiya da ‘yan bindiga a jihar.
A wani labarin mai nasaba da wannan, TRT Hausa ta ruwaito cewa a Juma’ar da ta gabata ’yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a ƙauyuka uku na Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da mutum fiye da 100, kamar yadda dagatai da mazauna yankunan suka tabbatar.
Dagacin Karamar Hukumar Birnin-Magaji, Alhaji Bala, ranar Asabar ya tattabar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa maharan sun yi dirar mikiya a ƙauyukan Gora, Madomawa da Jambuzu kuma waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da maza 38 da mata 67 da ƙananan yara da dama.
Ya ƙara da cewa, “Amma mutanen da aka sace suna iya fin haka yawa.”
Shi ma Aminu Aliyu Asha, dagacin ƙauyen Madomawa, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa gomman ’yan bindiga a kan babura ne suka kai musu hari inda suka yi ta harbe-harbe sannan suka sace mutane da dama.
“Wannan garkuwa da mutane da ’yan bindiga suka yi ta keta yarjejeniyar zaman lafiya da muka ƙulla da su. A watan Fabrairun da ya wuce, mun ba su maƙudan kuɗaɗe domin kada su kawo mana hari,” in ji shi.
Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara Yazid Abubakar, ya ci tura.
Sai dai Nusa Sani, wani mazaunin ƙauyen Madomawa, ya ce ’yan uwansa biyu na cikin waɗanda aka sace.
Kazalika shi ma Garba Kira ya ce cikin waɗanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su har da fasinjoji 15 na wata motar haya da ke kan hanyar zuwa ɗaya daga cikin ƙauyukan.
Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa waɗanda ke sace mutane a cikin gaguruwansu da ɗalibai da sauransu.
A watan jiya, Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Sha’anin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce akwai jagororin ’yan bindiga kimanin 300 a yankuna daban-daban da ke Arewacin ƙasar, lamarin da ya sake fitowa da girman matsalar tsaro, musamman a arewacin Nijeriya.