’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a iyakar Nijar da Najeriya
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewar an daɗe ba a kai hari ba.
’Yan bindiga sun kai hari a kan iyakar Nijar da Najeriya, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata wani ɗaya a garin Dambu da ke ƙaramar hukumar Bazaga a gundumar Birni N’Konni, sannan suka yi awon gaba dabbobi da dama a garin.
Sun kai harin ne a daidai lokacin da damina ke kankama a yankuna da daban-daban na Jamhuriyar Nijar.
- An ceto ’yan Najeriya 58 da aka yi safarar su zuwa Ghana
- Yadda mai tallan kifi ya sayar da zinaren sata N60m a Abuja
An dai jima ba a ji duriyar ’yan bindiga a kan iyakokin Nijar da Najeriya ba, inda suka afka wa al’ummar garin Dambu da ke cikin ƙaramar hukumar Bazaga.
Hakimin garin Dambu, Halidu Assoumane, ya ce maharan sun shiga garin da kusan ƙarfe 12 na daren ranar Asabar.
Ya ce sun shiga garin ne a kafa, kafin su buɗe wuta, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata wani da yake cikin mawuyacin hali yanzu haka a asibitin Galmi.
Ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da dukiya mai yawa da suka haɗa da raƙuma da shanu kafin jami’an tsaro su isa garin.
Kyaftin Abubakar Ali Shina, wanda shugaban tsaron yankin ne, ya buƙaci jama’a da su samar wa kansu ’yan sa-kai da za su ke taimaka musu wajen daƙile hare-haren ‘yan bindiga.