’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Sakkwato

Maharan sun kuma kwashe dabbobin masu yawa da ba a tantance adadinsu ba sannan suka tsere.

’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Sakkwato

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum shida tare da jikkata wasu biyar a wani hari da suka kai ƙauyen Lajinge da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa har zuwa kusan ƙarfe 2:20 na dare, lamarin da ya yi matuƙar razana al’ummar yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma kwashe dabbobin masu yawa da ba a tantance adadinsu ba sannan suka tsere.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan ba su yi garkuwa da kowa ba, sai dai sun kashe mutum shida, ciki har da wata matar aure, sai waɗanda suka jikkata da ke ci gaba da karɓar magani a asibiti.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ko wakilan yankin, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba.