’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace wasu a Kaduna

Mazauna yankin sun bukaci jami’an tsaro su tsaurara tsaro dom hana mahara kai musu farmaki.

’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace wasu a Kaduna

Aƙalla mutum biyar ne ’yan bindiga suka kashe tare da sace wasu da dama a ƙauyen Kallah Afogo, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar da Gwamnatin Jihar ba su fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.

Mazauna garin sun ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 11:15 na daren ranar Lahadi, inda suka ɓalle gidaje suka dinga ɗaukar mutane.

Aminiya ta gano cewa waɗanda aka kashe a ƙauyen na Kallah su ne Garkuwa Alfarma, Buhari Maidiga, Uba Auta, Yakubu Thomas Gaku, da Atabata Naallah.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, wanda ya bi sahun ’yan bindigar zuwa daji, sun gano shi tare kashe shi ta hanyar sare masa kai.

Har wa yau, ’yan bindigar sun kai hari yankin Bakin Pah da ke mazaɓar Maro, inda suka kashe mutum ɗaya sannan suka yi awon gaba da mutum shida.

Wani mazaunin garin mai suna Maigari Ben, ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara tsaurara tsaro a yankuna, tare da ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su.

Jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya ci tura, saboda wayarsa tana kashe zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas

Hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 — NBS