’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace wasu a Sakkwato

Maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da ba a san adadinsu ba.

’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace wasu a Sakkwato

Yan Bindiga sun kai hari cikin daren ranar Asabar har zuwa wayewar Lahadi, inda suka kashe mutum shida a garin Tudun Doki da ke ƙaramar hukumar Gwadabawa a Jihar Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewar ’yan bindigar sun shiga gari ne da misalin ƙarfe 1 na dare, inda suka buɗe wuta kan jama’a tare da yin awon gaba da wasu da ba a bayyana adadinsu ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce cewa tuni aka gano gawar mutum shida.

Harin dai na zuwa ne daidai lokacin da jama’a ke shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallar layya.

Rufai, ya ce garin Tudun Doki, gari ne mai nisa daga hedkwatar ƙaramar hukumar Gwadabawa, kuma abu ne mai matuƙar wuya a iya shiga yankin saboda rashin hanya.

Gwadabawa, na ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro musamman a Gabashi da Arewacin Sakkwato, inda sau da dama ’yan bindiga na kai hare-hare tare da kashe mutane da kuma sace wasu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta