’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a harin Jibiya
Wasu ’yan bindiga da ake zaton barayin shanu ne sun kashe mutum bakwai a harin da suka kai kauyen Shimfida a karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina. Maharan wadanda suka yi wa garin dirar mikiya da rana a Juma’ar da ya gabata, sun shiga garin dauke da bindigogi suna harbin kan mai uwa da wabi […]
Wasu ’yan bindiga da ake zaton barayin shanu ne sun kashe mutum bakwai a harin da suka kai kauyen Shimfida a karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina. Maharan wadanda suka yi wa garin dirar mikiya da rana a Juma’ar da ya gabata, sun shiga garin dauke da bindigogi suna harbin kan mai uwa da wabi inda jama’ar garin suka rika gudu zuwa daji. Malam Haruna Shimfida ya shaida wa Aminiya cewa, “Muna kyautata zato maharan barayin shanu ne da suka fito daga dajin Dunburum. Sun kashe mana mutane sun kuma kora shanu, bayan kone mana gidaje da ababen hawa.” Kakakin karamar Hukumar Jibiya, Alhaji Sa’adu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, akalla mutum bakwai ne suka rasu a yayin da mutum hudu ke kwance a babban asibitin Jibiya sanadin raunukan da suka samu a harin.
Ya ce, an kashe wasu daga cikin maharan, kuma ya ce komai ya lafa jama’a sun ci gaba da harkokinsu, sai dai ya ce, babu wanda aka kama. Wadanda Aminiya ta tattauna da su a garin da suka nemi a sakaya sunansu sun bukaci hukumomi su kara zage damtse don fatattakar barayin tunda an san maboyarsu kuma ba wannan ne karo na farko ba. Kakakin Hukumar Sibil Difens, Aliyu Jamilu BK ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro na hadin gwiwa ne suka shawo kan lamarin ta hanyar kai dauki, kuma suna ci gaba da bincike. Shi dai wannan daji na Dunburum yana iyaka da Zurmi ta Jihar Zamfara da Birnin Gwari a Jihar Kaduna sai karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.