’Yan bindiga sun kashe mutum 7 sun sace dabbobi a Bakori
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai wani jami’in rundunar tsaron al’umma ta CWC da gwamnatin Jihar Katsina, mai suna Jarma, wanda aka fi sani da Tukur Bunsuru.
Taswirar Jihar Katsina
Wasu ’yan bindiga sun kai hari garin Jargaɓa da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka kashe mutum uku tare da sace dabbobi masu yawa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Alhamis, lokacin da maharan suka mamaye garin tare da harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai wani jami’in rundunar tsaron al’umma ta CWC da gwamnatin Jihar Katsina, mai suna Jarma, wanda aka fi sani da Tukur Bunsuru.
Bayan harin Jargaɓa, maharan sun wuce zuwa ƙauyen Gidan Goje, inda suka sake kashe mutum huɗu.
- ’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun masu garkuwa a Kaduna
- Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 4 a Zamfara
Ko da yake ba su yi garkuwa da kowa ba, sun kwashe dabbobi masu yawa, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a tantance adadinsu ba.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa da jami’an tsaro suka fitar dangane da harin.
Ƙoƙarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin hukumomin tsaro domin samun ƙarin bayani bai yi nasara ba.