’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun raunata wasu a Kaduna

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta uffan kan faruwar harin ba.

’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun raunata wasu a Kaduna

Akalla mutum tara ne aka ruwaito cewa ’yan bindiga sun kashe a wani hari a kauyen Ungwan Dakwa da ke kusa da unguwar Dogon Dawa a Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Duk da cewa rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce uffan kan lamarin ba, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Gwari, Yahaya Birnin Gwari, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan bindigar sun dirar wa al’ummarsa ne da misalin karfe 2 na ranar Asabar, inda nan take suka bude wuta kan mutanen da ba su ji ba ba.

Ya ce wasu mutanen kauyen sun samu raunuka a harin, amma garzaya da su asibitocin da ke makwabtaka da Funtuwa a Jihar Katsina domin yi musu magani, yayin da akasarin mutanen kauyen suka tsere saboda fargabar kawo sabon hari .

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga.

Hare-hare da sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa na ci gaba da kamari tun bayan kammala zabe a watan Fabrairu da Maris.

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum 33 a wani hari da suka kai wani kauye da ke Kaduna a watan da ya gabata.

A farkon watan nan, an kuma yi garkuwa da yara ’yan makaranta 10 a Kaduna, ko da yake daga baya takwas sun yi nasarar tserewa makonni biyu da sace su.

Har wa yau, an kuma sace wasu limaman Katolika a jihar.

Sai dai a bangare daban-daban jami’an tsaro a jihar na ci gaba da yaki da ta’addanci kuma an samun kyakkyawan sakamako.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa