’Yan bindiga sun kashe mutum da raunata wani a Jos
Kwanaki kaɗan da suka gabata ma an kai irin wannan harin a daidai yankin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wani wanda har yanzu yana asibiti.
An kashe mutum guda yayin da wani kuma ya sami mummunan rauni biyo bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai a Sabon Gidan Kanar da ke Gundumar Gyel a ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Harin, wanda ya auku a daren ranar Alhamis, ya yi sanadiyyar mutuwar wani mai suna Mista Shedrack Dalyop, mai shekara 36, mazaunin Gundumar Kuru. Shi kuwa Mista Mang Davou mai shekara 32, mazaunin Gundumar Gyel, ya sami raunuka masu tsanani kuma a halin yanzu yana karɓar magani.
- Abdulsalami ya nemi ’yan Najeriya su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro
- Kotun Ƙoli ta halasta wa masu ta’ammali da tabar wiwi mallakar bindiga a Amurka
Kwanaki kaɗan da suka gabata ma an kai irin wannan harin a daidai yankin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wani wanda har yanzu yana asibiti.
Duk da haka, lamarin ya auku ne kwana huɗu kacal bayan da aka kai hari a Cibiyar Nazari da Tsare-tsare ta Kasa (NIPSS) da ke Kuru, ita ma a Jos ta Kudu, inda aka kashe wasu jami’an tsaro.
Da take mayar da martani kan lamarin, ƙungiyar Matasan Berom (BYM), ƙarƙashin jagorancin lauya Dalyop Solomon Mwantiri ta bayyana cewa, wadannan hare-hare suna nuna yadda yanayin tsaro ke ƙara tabɓarɓarewa ga mazauna yankin.
ƙungiyar ta ce: “BYM tana kira ga rundunar Operation Enduring Peace da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan harin, su kamo waɗanda suka aikata laifin, kuma su tabbatar an gurfanar da su a gaban shari’a.
ƙungiyar tana miƙa ta’aziyyarta tga iyalan marigayi Shedrack Dalyop, sannan tana addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga Mista Mang Davou.
Muna shawartar mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kasance masu sanya idanu, kuma su kasance masu bin doka yayin da hukumomin tsaro ke ɗaukar ƙwararan matakai domin shawo kan matsalar tsaron da ke ƙara muni.
Kada a bari ci gaba da kai hari da karkashe bayin Allah da ba su san hawa ba ba su san sauka ba ya ci gaba da faruwa.”
Sandan Jihar Filato (PPRO), Alfred Alabo bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa ba.