’Yan bindiga sun kashe mutum da sace shanu fiye da 300 a Kano
Kansilan mazaɓar Mainika, Auwal Abdussalam Barau, ya bayyana cewa maharan sun zo ne da muggan makamai, kuma ana zargin sun tsallako ne daga maƙwabciyar jihar, wato Jihar Katsina.
Wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani makiyayi sannan suka yi awon gaba da shanu fiye da 300 a unguwar Mainika da ke ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
An bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne a yammacin ranar Laraba.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kansilan mazaɓar Mainika, Auwal Abdussalam Barau, ya bayyana cewa maharan sun zo ne da muggan makamai, kuma ana zargin sun tsallako ne daga maƙwabciyar jihar, wato Jihar Katsina.
- AbdulSamad Rabi’u ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka
- Ranar Asabar Gwamnatin Katsina za ta aurar da mutane 1000
Ya ce: “Sun zo ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Laraba, inda suka sace shanu fiye da 300, tare da kashe wani makiyayi guda wanda ya yi ƙoƙarin nuna musu turjiya.
“Bayan harin, an tura dakarun sojoji da ’yan banga. Sun bi sawun maharan inda daga ƙarshe suka yi nasarar ƙwato shanu fiye da 100.
“Wannan ba shi ne karo na farko da suke kai hari a wannan yankin ba. Akwai lokacin da suka sace wata matar aure da wani matashi, sannan suka sake dawowa suka sace wani dattijo. Wannan shi ne hari na uku da aka kai yankinmu.”
Kansilan ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ba su tabbacin cewa za a ƙwato sauran shanun da suka rage. Daga nan ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta yi la’akari da kafa sansanin soja a yankin domin taimakawa wajen daƙile hare-hare a nan gaba.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta sanar da cewa jami’anta, tare da haɗin gwiwar dakarun haɗin gwiwa na soja (JTF), sun ƙwato shanu 67, jaki ɗaya, da kuma tunkiya ɗaya daga hannun ɓarayin yayin wani samame na gaggawa.
A cewar Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, rundunar ta samu ƙwararan bayanan sirri ne a ranar 6 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 6:15 na yamma, cewa wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne sun kai hari ƙauyukan da ke kewayen Gwarzo da sauran yankuna maƙwabta.
Ya ƙara da cewa: “An tura jami’an haɗin gwiwar ’yan sanda da dakarun JTF, kuma da ganin jami’an tsaro, sai waɗanda ake zargin suka buɗe musu wuta. An fi ƙarfin su, wanda hakan ya tilasta musu barin dabbobin da suka sata suka tsere zuwa wajen jihar.”