’Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Katsina, sun sace iyalansa

Maharan sun yi awon gaba da matan mamacin biyu da kuma ‘yarsa guda ɗaya.

’Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Katsina, sun sace iyalansa

’Yan bindiga sun kashe Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Katsina, Alhaji Surajo Leader, tare da wasu mutum biyu a Ƙaramar Hukumar Kusada a Jihar Katsina.

Maharan sun kai harin ne a daren ranar Asabar, garin Mai Rana da ke cikin Kusada.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matan Alhaji Surajo guda biyu da ’yarsa, wadda ɗalibar jami’a ce.

Tuni aka yi jana’izar Alhaji Surajo bisa koyarwar Addinin Musulunci, yayin da tsoro da fargaba suka mamaye yankin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce ’yan sanda sun yi gaggawar ɗaukar mataki tare da yin musayar wuta da ’yan bindigar, wanda hakan ya sa suka tsere.

A yayin arangamar, ’yan sanda sun gano ɗaya daga cikin motocin ’yan bindigar, wanda a cikinra ne suka ceto ɗaya daga cikin matan mamacin da suka sace.

ASP Aliyu, ya tabbatar wa jama’a cewa suna ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda maharan suka sace.

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar da su ke bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gano maɓoyar ’yan ta’addan.