’Yan bindiga sun kashe sojoji 11 a dajin Birnin Gwari

Wadansu ’yan bindiga a sun kashe sojoji 11 a matsuguninsu da ke Kamfanin Doka a kan titin Funtuwa da ke yankin Maganda a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna a daren Talatar da ta gabata. Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kuma raunata sojoji uku a lokacin harin. Babu bayanin ko mahara nawa […]

’Yan bindiga sun kashe sojoji 11 a dajin Birnin Gwari

Wadansu ’yan bindiga a sun kashe sojoji 11 a matsuguninsu da ke Kamfanin Doka a kan titin Funtuwa da ke yankin Maganda a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna a daren Talatar da ta gabata.

Rahotanni daga yankin sun ce ’yan bindigar sun kuma raunata sojoji uku a lokacin harin. Babu bayanin ko mahara nawa aka kashe a lokacin gumurzun amma an ce su ma sun samu hasarar rayuka a cikinsu.

Wata majiyar Aminiya a garin na Birnin Gwari (an sakaya ta), ta ce maharar sun kai harin ne a kan babura da misalin karfe 10 na daren Talata.

“Sun raunata sojoji uku sannan kusan 11 sun rasu. Kuma sun raunata ’yan sintirin garinmu da suka je wajen da nufin kai-dauki. Kodayake babu wanda ya rasa ransa daga cikin ’yan sintirin amma mutum tara sun samu raunuka sakamakon harbinsu da aka yi, inda yanzu haka suke asibiti suna jinya,” inji shi.

Wadansu na ganin kamar harin na ramuwar gayya ce ga kisan Buharin Daji da aka yi a Jihar Zamfara a makon jiya.

Aminiya ta nemi jin ta bakin Kakakin Rundunar Sojoji ta daya da keKaduna, Kanar Muhammad Dole, inda ya ce sun rigaya sun shiga daji domin binciken abin da ya faru. Don haka ya ce a ba shi lokaci domin fitar da cikakkiyar sanarwa a kan lamarin.