’Yan bindiga sun kashe sojoji 2 a Neja
Gwamnan ya ziyarci sojojin da ke jinya a Asibitin Ibrahim Badamasi Babangida a Minna.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar wasu sojoji biyu a wani hari da ’yan bindiga suka kai yankin Kagara a Jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fito daga Fadarsa da ke Minna, babban birnin jihar.
- Hana mu Dala ta jefa Naira a mawuyacin hali — ’Yan canji
- Ganduje ya gargadi gwamnoni su guji raban kan jama’a
Sanarwar ta ce gwamnan ya ziyarci sojoji 12 da ke jinya a Asibitin Ibrahim Badamasi Babangida a Minna wadanda suka samu rauni a yayin harin.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito gwamnan na cewa an garzaya da wasu sojojin zuwa Kaduna domin kula da lafiyarsu.
Ya kuma ce ’yan bindiga da dama sun rasa rayukansu yayin artabu da sojojin sai dai bai bayyana adadinsu ba.