’Yan bindiga sun kashe sojoji 2 da dan sanda a NIPPS Kuru
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta ce sojoji da ɗan sandan sun rasa rayukansu ne a lokacin musayar wuta da ’yan bindigar
NIPSS Kuru
’Yan bindiga sun kai hari a Cibiyar Nazari da Tsare-tsare ta Kasa (NIPSS) da ke Kuru, Jihar Filato a daren Litinin, inda suka kashe sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya.
Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na cibiyar, Dakta Osime Samuel, ya sanar da hakan a safiyar ranar Talata, amma bai bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ko yadda abin ya faru ba.
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta ce sojoji da ɗan sandan sun rasa rayukansu ne a lokacin musayar wuta da ’yan bindigar yayin da suke tsaron wurin mazaunin ma’aikatan.
- Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi
- Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano
- Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi
“Da rana, masu tsaron unguwa ne ke kula da mazaunin ma’aikatan. Amma da dare, sojoji da ’yan sanda ake turawa . Ana kyautata zaton ’yan bindigar sun kai hari ne a gidajen ma’aikatan da suka aika musu da saƙon neman kuɗi a baya,” in ji majiyar.
Wakilinmu ya ya ruwaito cewa an kai gawarwakin jami’an tsaron da abin ya rutsa da su zuwa dakin ajiye gawa, kuma waɗanda abin ya rutsa da su suna tsaron mazaunin ma’aikatan cibiyar.
Dakta Osime Samuel ya ce : “Cibiyar Nazari da Tsare-tsare ta Kasa, Kuru, tana sanar da jama’a cewa wani lamari na tsaro ya faru a kusa da cibiyar kafin wayeawr garin yau.”
Samuel ya ƙara da cewa an shawo kan lamarin ta hanyar gaggawar da jami’an tsaro suka yi wurin kawo dauki, kuma “a halin yanzu babu wani barazana ga tsaron mahalarta, ma’aikata, mazauna ko kewayen cibiyar. Ayyuka na ci gaba kamar yadda aka tsara.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai hari ne a gidajen Mukaddashin Daraktan Nazari, Barista Nima Salman-Mann, da kuma Farfesa Haruna Dabin.
Majiyoyi sun ce waɗannan ma’aikatan sun samu saƙonnin barazana da aka liƙa a ƙofofinsu a ranar Asabar, inda aka nemi su biya kuɗi har Dala 100,000 da Naira miliyan 15 kowannensu, kuma sun riga sun sanar da hukumar cibiyar kan lamarin.
Hukumar gudanarwar NIPSS ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun fara bincike don gano ainihin yadda lamarin ya faru.
“Cibiyar NIPSS tana aiki tare da hukumomin da suka dace kuma za ta bayar da sahihin bayani da zarar ya samu. Muna roƙon jama’a da kafafen yaɗa labarai su dogara da sanarwar hukuma da jami’an tsaro.
“Shugabancin NIPSS ya yi tsayuwar daka wajen tabbatar da tsaron dukkan membobin cibiyar, kuma yana yaba wa ƙwarewar jami’an tsaro da hukumomin da suka kawo dauki wajen shawo kan lamarin,” in ji Dakta Samuel.