‘Yan bindiga sun kashe Sojoji biyu, sun kone Kotu a Anambra
Maharan sun dauki tsawon lokaci suna musayar wuta da sojojin.
Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe sojoji biyu a wata musayar wuta da suka yi daren Lahadi a rukunin gidaje na 3-3 da ke yankin Nkwelle Ezunaka, kusa da Onitsha a Jihar Anambra.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun harbe sojoji biyu a yayin harin.
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Daukar Doka A Hannu A Mahangar Shari’a
- Amarya da ango da wasu mutum 40 sun kwanta bayan cin abincin biki a Afghanistan
A cewarsa, an fara harbe-harben ne da misalin karfe 10 na dare, wanda ya dauki tsawon sa’o’i ana yi.
Kazalika, an gano cewa maharan sun kai wa sojoji hari yayin da suke cikin wani gidan.
A cewar wata majiya, lamarin ya jefa yankin cikin firgici yayin da harbe-harbe suka ci gaba da ta’azzara.
Majiyar ta ce, “Gaskiya ne, jiya da daddare mahara sun farmaki sojojin da suke tsare mu da misalin karfe 10 na dare. An dauki tsawon sa’o’i uku ana musayar wuta. An kashe sojoji biyu.”
Aminiya ta gano cewa maharan sun kuma kai wani farmaki yankin GRA da ke Onitsha, inda nan ma suka yi harbe-harbe.
A wani labarin kuma wasu mahara sun kona sakatariyar Karamar Hukumar Idemili ta Arewa da ke Ogidi da kuma wata kotun Majistare da ke yankin.
Wata majiya ta ce maharan sun shiga harabar ne ranar Lahadi da daddare, inda suka kona takardu da wasu kayayyaki a cikin sakatariyar kafin su kone ginin baki daya.
Bidiyo da hotuna da ke yawo a Intanet sun nuna yadda ginin ya kone, kazalika sun kone motocin da ke ajiye a cikin sakatariyar karamar hukumar.
Rundunar ‘yan sandan Jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta danganta lamarin ga wadanda ba a san ko su waye ba.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya ce, “Lamarin ya faru kuma mun tura mutanenmu wurin domin a daidaita al’amura.”
“A yanzu haka, an kashe wutar, kuma an samu kwanciyar hankali a yankin,” in ji Ikenga.
Ya kuma tabbatar da harin da aka kai wa sojojin, a yankin Nkwelle Ezunaka da ke Onitsha, amma bai yi karin haske game da asarar rayuka ba.