’Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban APC a Kebbi
Tun kusan makonni uku da suka gabata ne Malam Maibarga ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Koko/Besse a Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi tun a farkon watan Yuni.
An dai yi garkuwa da marigayin ne tare da abokinsa, Malam Muhammadu Maibarga, malamin addini na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS).
- PRP ta yi fatali da shirin kafa ’yan sandan jihohi
- Venezuela na ci gaba da samun tallafi bayan mummunar girgizar ƙasa
Aminiya ta ruwaito cewa, tun kusan makonni uku da suka gabata ne Malam Maibarga ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.
Kafin rasuwarsu, ’yan bindigar sun fitar da wani bidiyo da ya nuna mutanen biyu suna tsare a cikin daji.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce har yanzu suna gudanar da bincike kan rasuwar tsohon shugaban jam’iyyar.