’Yan bindiga sun kashe tsohon soja, sun sace wata mata a Nasarawa

Maharan sun harbe tsohon sojan har lahira yayin da yake ƙoƙarin ceton matar da suka sace.

’Yan bindiga sun kashe tsohon soja, sun sace wata mata a Nasarawa

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wani tsohon soja tare da sace wata mata a wani hari da suka kai wata unguwa da ke iyakar Jihar Nasarawa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A cewar masanin harkar tsaro, Zagazola Makama, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:45 na daren ranar Juma’a a kusa da yankin Jikwoyi.

Rahoton ya ce maharan sun kutsa cikin gidan Silas Orite mai shekara 46, inda suka yi garkuwa da matarsa, Bukola Oluwatoyin Silas mai shekara 40, suka tafi da ita.

Wani tsohon Sojin Najeriya, Reuben Yelwa (mai ritaya) mai shekara 61, ya garzaya wajen domin taimaka wa iyalan da aka kai wa harin.

Sai dai ‘yan bindigar sun harbe shi har lahira.

Bayan faruwar harin, ‘yan sanda sun isa wajen, inda suka fara bincike kan lamarin.

Hukumomin tsaro sun ce sun ƙara ƙaimi wajen ceto matar da aka yi garkuwa da ita cikin ƙoshin lafiya, tare da farautar waɗanda suka kai harin.

Sun kuma ƙara tsaurara tsaro a yankin domin daƙile aukuwar irin wannan hari.