’Yan bindiga sun kashe uban garin Dalijan a Sakkwato
Garin Dalijan yana da iyaka da Tangaza da Gudu, yankunan da Lakurawa suka matsawa da hare-hare.
’Yan bindiga sun kai hari garin Dalijan a Ƙaramar Hukumar Binji, a Jihar Sakkwato, inda suka kashe uban garin, Alhaji Ibrahim Magaji Tanko.
Bayan kashe shi, maharan sun sace shanu, awaki, tumaki da kaji, tare da kayan abinci masu yawa.
- Yadda yaron shago ya hallaka ubangidansa a gaban mahaifiyarsa a Gombe
- Bayan shekara 12 an kama wanda ake zargi da kashe jami’an NDLEA 3
Ƙaramar Hukumar Binji tana iyaka da Tangaza da Gudu, yankunan da Lakurawa suka matsawa da kai hare-hare.
Wannan lamari ya haddasa tashin hankali da firgici a yankin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Binji, Alhaji Dikko Nabunkari, ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali.
Ya ce: “Allah Ya gafarta masa, ya bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.”