’Yan bindiga sun kashe wanda ya aure budurwar shugabansu a Kaduna

Tun bayan harin da aka kashe matashin aka nemi amaryar aka rasa

’Yan bindiga sun kashe wanda ya aure budurwar shugabansu a Kaduna

Wani dan bindiga a Jihar Zamfara.

Bayanai daga Jihar Kaduna na nuni da cewa ’yan bindiga sun harbe dan Sarkin Hausawan Janjala ne saboda ya aure budurwar shugabansu.

Shaidu sun bayyana cewa bayan tarewar amaryar ne ’yan bindiga suka yi dirar mikiya a gidan dan Sarkin Hausawan Janjala, Safiyanu Ibrahim, suka harbe shi a gaban mahaifiyarsa.

Marigayi Safiyanu ya auro amaryar tasa wadda suka hadu a garin Kagarko a matsayin matarsa ta biyu ce daga Jihar Zamfara.

A ranar Asabar 18 ga Mayu, 2024 ne ’yan bindiga suna kutsa gidansa suka hallaka shi tare da kaninsa mai suna Nasiru sannan suka tsere.

Shaidu sun ce mahaifiyar matasan ta yi ta magiya ga maharan su bar ’ya’yan nata da ransu, amma suka shafa wa idanunsu toka suka harbe su a kan idonta.

Wani dan uwansu na dangi ya shaida wa wakilinmu cewa Safiyanu da amaryar tasa, wadda ’yar Zamfara ce, sun fara haduwa ne a garin Kagarko inda suka fara soyayya.

Daga bisani saurayin nata wanda shugaban ’yan bindiga ne ya kira marigayi Safiyanu a waya ya gargade shi cewa ya rabu da ita.

Ya ce, “Bayan auren amaryar ta ki tarewa a dakin mijinta sai da wani abokinsa ya sanya baki.

“Washegarin tarewar ne ‘yan bindiga suka je gidan suka kashe shi, kuma tun a ranar aka nemi amaryar a gidan aka rasa.

“Har yanzu ba a san inda take ba, wanda hakan ya haifar da zargi,” in ji shi.

Wani dan uwan mamacin ya bayyana cewa an daura auren marigayi Safiyanu da amaryar tasa ne a Jihar Zamfara kimanin mako guda kafin a kashe shi.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani game da lamarin daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, amma har aka kammala hada wannan rahoton jami’in bai amsa ba.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki