`Yan bindiga sun kashe wani da yin garkuwa da matarsa a Kaduna
Rahotanni daga unguwar Rigasa a safiyar yau Alhamis na bayyana cewa, wasu da ake zargin `yan bindiga ne sun kashe wani mutum mai suna Abdul’azeez da kuma yin garkuwa da matarsa. Majiyarmu ta gano cewa, lamarin ya faru ne da safiyar yau lokacin da `yan bindigar suka shiga cikin gidan Abdul’azeez da ke yankin Karshen […]
Rahotanni daga unguwar Rigasa a safiyar yau Alhamis na bayyana cewa, wasu da ake zargin `yan bindiga ne sun kashe wani mutum mai suna Abdul’azeez da kuma yin garkuwa da matarsa.
Majiyarmu ta gano cewa, lamarin ya faru ne da safiyar yau lokacin da `yan bindigar suka shiga cikin gidan Abdul’azeez da ke yankin Karshen Kwalta a unguwar Rigasa da ke Kaduna.
Wani makwabcin Abdul`azeez da ya bukaci a sakaya sunansa ya sanarwa majiyarmu cewa, wannan abin da ya faru ya razana mazauna unguwar kuma suna cikin fargaba.