‘Yan bindiga sun kashe wani mai unguwa a Kaduna

’Yan bindigar sun riƙa shiga gida-gida suna ɗiban waɗanda tsautsayi ya faɗa kansu.

‘Yan bindiga sun kashe wani mai unguwa a Kaduna

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Gefe da ke unguwar Kallah a masarautar Kufana ta Ƙaramar Hukumar Kajuru, inda suka kashe mai unguwar ƙauyen da wani mutum guda.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutanen ƙauyen da suka haɗa da mata da ƙananan yara a lokacin da suka afka wa al’ummar garin da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar daren ranar Alhamis.

Wani shugaban unguwar kuma ɗan uwan ​ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Markus Danja ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa an harbe mutanen biyu da aka kashe, ciki har da mai unguwar Mista Emmanuel Idan.

“Su [maharan] na shigowa ƙauyen suka fara harbe-harbe kuma babu daɗewa suka yi wa mazauna ƙawanya.

“Mutanen da suka hangi shigowar su sun ranta a na kare domin neman mafaka.

“Sai dai abin takaicin shi ne mai unguwar ƙauyen namu yana cikin waɗanda suka yi yunƙurin tserewa amma kafin ya samu mafaka sun harbe shi.

“Sai kuma ɗaya mutumin da suka kashe sun harbe shi ne har cikin ɗakinsa sannan suka tafi da matarsa.

“‘Yan bindigar sun riƙa shiga gida-gida suna ɗiban waɗanda tsautsayi ya faɗa kansu,” in ji shi.

Shugaban unguwar ya bayyana cewa suna ƙoƙarin tattara adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ko kuma suka ɓace, yana mai cewa matan ɗan uwansa da ‘ya’yansa ma an neme su an rasa.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta shiga ƙungiyar BRICS

Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai