’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

’Yan fashin daji sun kashe ’yan banga huɗu tare da yin awon gaba da wani mai Unguwa a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

‘Yan banga

’Yan fashin daji sun kashe ’yan banga huɗu tare da yin awon gaba da wani mai Unguwa a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

’Yan fashin dajin sun kuma ƙona babura bakwai tare da a sace wasu biyar a harin da suka kai yankin Unguwar Agyaro da ke yankin Kakangi.

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Kishin Yankin Birnin Gwari, Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar cewa “’yan bindigar sun yi awon gaba da mutane huɗu a yankin Maraban Agyaro da ke kan hanyar Kakangi zuwa Birnin Gwari.”

Yahaya Musa DanSalio, ɗan majalisa mai wakiltar yankin Kakangi a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya ce ya samu labarin mutuwar ’yan banga uku da ɓacewar na huɗun nasu.

“Muna ƙoƙarin tattara alƙaluman, amma na sanar da gwamnati game da lamarin.

“Na ji cewa maharan sun yi abin ga ba da Mai Unguwar yankin Rafin Gora tun ranar Juma’a.”