‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 2 a Katsina
Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai wani sabon hari inda suka kashe jami’an ‘yan sanda biyu Bashir da Ibrahim masu mukamin sufeta a kauyen Shekewa a unguwar Magaji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina. An dai tura jami’an ‘yan sandan ne yankin daga ofishin hukumar ‘yan sanda na Batsari sanadiyyar […]
Rahotanni na bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai wani sabon hari inda suka kashe jami’an ‘yan sanda biyu Bashir da Ibrahim masu mukamin sufeta a kauyen Shekewa a unguwar Magaji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
An dai tura jami’an ‘yan sandan ne yankin daga ofishin hukumar ‘yan sanda na Batsari sanadiyyar hare-haren da ‘yan bindigar suke kaiwa kauyen.
Rahoton ya kara da cewa, ‘yan bindigan sun shiga garin ne akan babura sama da guda 50 inda suka yi ta harbin jama’ar garin.