’Yan sandan sun kashe dan bindiga daya, wasu biyu kuma sun samu raunin harbi a musayar wutar, amma duk da haka sun kwashe bindigogin ’yan sandan.
Majiyarmu ta ce an cafke ’yan bindigar da suka samu runin harbi an kai su wani asibiti, kuma ana ci gaba da bincikea kansu.
Majiyar ta ce daga baya an yi nasarar kwato bindigogi shida daga maboyar maharan a cikin dajin da ke yankin.
Maharan sun kai wa jami’an tsaron hari ne da asuba a kusa da Kasuwar Agbor, inda ’yan sandan kwantar da tarzoma sukan kafa shingen bincike.
’Yan sanda sun kafa shingen bincikenne domin magance ayyukan masu garkuwa da mutane da ke bin kauyukan yankin suna garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Jami’an tsaron suna tafiya a cikin motarsu ta aiki ne maharan suka yi musu kwanto bauna suka bude musu wuta, amma wani dan sanda daga cikinsu da yake kan babur ya yi dauki ba dadi da maharan, har suka tsere cikin daji da bindigogi hudu na ’yan sanda.
Daga bisani ’yan banga suka yi shara a dajin, inda suka gano maboyar bata-garin, suka kwato bindigogi shida.
Shugaban ’yan bangar yankin, Ibukun Dogo, ya ce sun ga gawarwakin ’yan sanda uku a wurin da suka kai dauki bayan an yi musu kiran gaggawa.
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, kan lamarin, amma ya ce ba su samu rahoton ba a hukumanci.