’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 9 a Pakistan
Maharan sun kai wa jami’an hari ne yayin da suke tsaka da aiki a wajen gina wata madatsar ruwa.
Wasu ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda tara, yayin da ake zargin wasu da dama sun ɓace bayan wani hari da aka kai wani wajen binciken ababen hawa da ke tsaron aikin gina madatsar ruwa a lardin Balochistan da ke Kudu Maso Yammacin Pakistan.
Wani babban jami’in gunduma, Abdul Qudoos, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa an kai harin ne kan wajen binciken da ke ba da tsaro ga aikin madatsar ruwan Mangi.
- Babu dalilin gaggauta yanke shawara kan makomata — Ronaldo
- Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz
“Jami’an ’yansanda tara sun mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan harin da aka kai kan wajen binciken da ke tsaron aikin madatsar ruwan Mangi,” in ji shi.
Mai magana da yawun gwamnatin lardin ya tabbatar da adadin waɗanda aka kashe.
Ya bayyana cewa daga cikin mamatan akwai manyan jami’an ’yan sanda daga ofisoshi daban-daban, inda ya kuma ɗora alhakin harin kan mayaƙa masu iƙirarin jihadi.
A wata sanarwa, kakakin gwamnatin Balochistan, Shahid Rind, ya ce jami’an rundunar sa-kai, ’yan sanda da masu yaƙi da ta’addanci sun kai farmakin haɗin gwiwa, inda suka samu nasarar fatattakar maharan.
Pakistan ta daɗe tana fama da matsalar ’yan tawaye masu neman ɓallewa a Balochistan, inda mayaƙan ke kai hare-hare kan jami’an gwamnati da kuma ayyukan zuba jari da gine-ginen manyan ababen more rayuwa a lardin mai arzikin ma’adinai da ke kan iyakar Afghanistan da Iran.
Harin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren mayaƙa a yankunan kan iyakar Pakistan.
Islamabad na zargin cewa suna samun mafaka ne a Afghanistan. Sai dai hukumomin Afghanistan sun sha musanta zargin.
A cikin watannin baya, Pakistan ta kai hare-haren sama a wasu sassan Afghanistan, inda ta ce tana kai wa mayaƙa farmaki.
Sai dai gwamnatin Taliban da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.