’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Anambra

’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda biyu har lahira a yankin Nnewi

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Anambra

’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda biyu har lahira a yankin Nnewi da ke Jihar Anambra.

Maharan sun hallaka ’yan sanadin ne ta hanyar buɗe musu wuta tare da jefa abin fashewa a cikin motarsu ne.

’Yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suke gudunar da wani bincike a yankin, a cewar kakakin ’yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun fara farautar maharan domin kamo su da tabbatar da sun girbi sakamakon wannan aika-aika.

Ya kuma buƙaci jama’a da su taimaka wa rundunar da bayanai da za su taimaka domin kamo bata-garin.

Yadda ƙananan yara ke zaman kurkuku ba tare an da kai su kotu ba

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines