‘Yan bindiga sun kona mutum 16 ‘yan gida daya a Kaduna

Mutum 16 ‘yan gida daya sun kone kurmus bayan ‘yan bindiga sun banka musu wuta a kauyen Bakali da ke lardin Fatika Karamar Hukumar Giwa a jihar Kaduna. Wakilinmu ya samu rahoton cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin da misalign karfe 4:00 na yamma ranar Talata, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da […]

‘Yan bindiga sun kona mutum 16 ‘yan gida daya a Kaduna

Mutum 16 ‘yan gida daya sun kone kurmus bayan ‘yan bindiga sun banka musu wuta a kauyen Bakali da ke lardin Fatika Karamar Hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wakilinmu ya samu rahoton cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin da misalign karfe 4:00 na yamma ranar Talata, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi tare  da kona gidajen jama’a, matoci, babura da kuma buhunan abinci.

Wani dan gidan da ya tsallake rijiya da baya ya ce ‘yan bindigar sun kulle iyalan a cikin gidansu sannan suka banka wa gidan wuta.

Wani mazaunin garin mai suna Alhaji Sani Bakali, ya ce ’yan bindigar sun kai 100 da suka shiga unguwar suka tarwatsa jama’a da dama.

Cikakken rahoton na nan tafe.