’Yan bindiga sun kona uwa da ’ya’yanta da ransu a Sakkwato

’Yan bindiga sun kona wata uwa da ’ya’yanta tare da surukarta da ransu a cikin daki a Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun kona uwa da ’ya’yanta da ransu a Sakkwato

’Yan Bindiga bindiga sun kona wata uwa da ’ya’yanta biyu tare da matar danta da ransu a Jihar Sakkwato.

’Yan ta’adda sun yi wannan aika-aika ne a wani hari da suka hallaka mutane 12 suka sace wasu mata uku a kauyen Kurya da ke Karamar Hukumar Rabah a daren Lahadi.

Wani mazaunin kauyen, Yusuf Garba, ya ce “Akwai wata da aka kone ta da ranta tare da ’ya’yan biyu da surukarta a cikin daki.”

Yusuf ya ce daga cikin matan da aka yi garkuwa da su akwai wadda ’yan bindigar suka kone mijinta da ransa.

Ya ce daga bisani sojoji sun kawo dauki an yi musayar wuta kuma “Muna kyautata zaton sojoji sun kakkashe su, saboda mun ga jini a wuraren da suka ajiye motoci da baburansu, ko da yake dauke gawarwakinsu suke yi.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP, Ahmed Rufa’i ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai, amma ya ce suna ci gaba da tattara alkaluma.

A ranar Alhamis da Asabar da suka gabata, idan ba a manta ba, sojoji sun ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su a Dajen Gundumi da ke gabashin Jihar Sakkwato.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa an kashe ’yan bindiga da dama a wadancan samame.

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka