’Yan bindiga sun lafta wa al’ummomi 16 sabbin haraji a Sakkwato
Bayan girbi, ana tilasta wa manoma ba wa ’yan bindigar wani kaso na amfanin gonarsu kafin a ba su damar adana amfanin gonar a rumbunansu
Wasu manoma a gona
Mazauna akalla ƙauyuka 26 a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato sun fara tara kuɗi domin biyan sabon harajin da ‘yan bindiga suka ƙaƙaba musu kafin noma gonakinsu a daminar bana.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa ko halaka duk wanda suka gani yana aikin gona kafin cikar wa’adin, a daidai lokacin da ake shirin fara ayyukan noma na damina.
Sun ƙara da cewa, ƙungiyoyin ‘yan bindigar sun ba su wa’adin kwana uku, tare da gargaɗin cewa manoma kada su kuskura su shiga gonakinsu har sai an biya kuɗaɗen harajin da aka ɗora wa ƙauyukan da abin ya shafa.
Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Garin Faji, Cina Barka, Zululu, Dan Gari, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga, Dan Kware, Garje, Dogon Faru, Son Allah, Garin Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin Labo, Zango, Kaifin Aska, Tsauna Dogo, Tudun Wada, Rambadawa, Ga Itace, Nasarawa da kuma Garin Idi.
- Zulum ya bai wa sojoji kyautar motocin yaƙi, ya tallafa wa ’yan gudun hijira
- Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno
Wani mazaunin yankin ya ce ’yan bindigar ya ce, “’Yan bindigar sun ba al’ummomin wa’adin kwana uku, suna masu cewa babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin. Duk wanda aka kama yana noma za a kashe shi ko kuma a sace shi, kuma ba za a sako shi ba sai an biya kuɗin fansa na Naira 500,000.”
Ya ƙara da cewa mazauna yankin sun riga sun fara tara kuɗaɗe domin cika buƙatun ’yan bindigar.
Wani mazaunin ƙauyen Zululu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa aranar Juma’a ne lokacin da ya samu labarin wannan lamari.
Ya ce, “An sanar da mu cewa ’yan bindigar sun dakatar da ayyukan noma na tsawon kwana uku har sai ƙauyukan sun biya harajin da suke karɓa a kowace shekara.
“Sun ce da sun so bari mutane su je gonakinsu sannan su kashe wasu su kuma yi garkuwa da wasu, amma sun fi son a ba su kuɗi. A cewarsu, jami’an tsaro suna kwace musu dabbobinsu, don haka ba za a yi noma ba har sai an biya harajin.”
Ya ce ana sa ran sarakunan gargajiya da malamai daga ƙauyukan da abin ya shafa za su gana da ’yan bindigar domin tantance adadin kuɗin da kowace al’umma za ta biya kafin a ci gaba da noma.
A cewarsa, shekaru da dama ke nan ’yan bindiga suna tilasta wa al’ummomin yankin irin waɗannan biyan kuɗaɗe.
Ya ce, “Muna biyan kuɗi kafin shuka, sannan wani lokaci bayan duk wata biyu ko uku. Ko mun biya yanzu, za su iya dawowa bayan wata uku su ce ba za a girbe gero ba har sai an sake biyan wani haraji.
“Tsakanin Naira miliyan huɗu zuwa miliyan shida sune karɓa daga kowace al’umma. Mazauna ƙauyuka na bayar da gudunmawa gwargwadon ƙarfinsu. Wasu gidaje na bayar da Naira 1,500 ko 2,000, yayin da a wasu ƙauyukan manoma ke bayar da har Naira 5,000 kowannensu, gwargwadon yawan al’ummar ƙauyen.”
Wata majiya daga Garin Idi da ke zaune a garin Sabon Birni a halin yanzu, wadda ta ziyarci ƙauyen a ranar Juma’a domin jajantawa bayan an sace kusan mutum 20 da safiyar ranar, ta tabbatar da cewa al’ummomin da abin ya shafa sun fara tara kuɗin biyan harajin.
Majiyar ta yi zargin cewa lokacin da ’yan bindigar suka ga ana jinkirin tara kuɗin, sai suka kai hari Garin Idi inda suka yi garkuwa da kusan mutum 20 a ranar Juma’a.
Ta ce, “Daga baya sun sanar da shugabannin al’umma cewa dole ne a biya Naira 600,000 kafin a sako mutanen. Da aka tara kuɗin aka biya, sun sako mutanen a ranar Juma’a.”
Majiyar ta ƙara da cewa, “Har zuwa yanzu akwai mutum biyar da ke tsare a hannunsu. Sun ce ba za su sake su ba har sai an biya harajin. Ko bayan an yi noma ma, za su iya hana mutane girbi su ce sai an sake biyan wasu kuɗaɗe.”
Ta kuma yi zargin cewa bayan girbi, ana tilasta wa manoma ba wa ’yan bindigar wani kaso na amfanin gonarsu kafin a ba su damar adana amfanin gonar a rumbunansu.
Ta ce, “A kowace shekara bayan girbi, suna karɓar wani kaso daga amfanin gonar manoma kafin su ba su damar ajiye amfanin gonarsu. Wannan ya zama wani nauyi da ake ci gaba da ɗora wa al’ummominmu.”
Wakilinmu tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, amma jami’in ya ce rundunar ba ta da masaniya kan lamarin.
Ya ce, “Ba mu da labarin faruwar irin wannan. A mafi yawan lokuta, al’ummomi ba sa kai irin waɗannan rahotanni ga hukumomin tsaro.”
Ƙoƙarin jin ta bakin Gwamnatin Jihar Sakkwato bai yi nasara ba. Saƙonnin tes da na WhatsApp da aka aika wa mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, da kuma Mashawarcin Gwamna Kan Harkokin Tsaro, Kanar Ahmad Usman mai ritaya, domin jin martaninsu kan zarge-zargen, ba a samu amsa daga gare su ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.