’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato

’Yan bindigar sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba.

’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato

‘Yan bindiga

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba.

Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin.

Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Rufa’i ya ce, rundunar ’yan sandan tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, suna aiki tuƙuru don ganin an sako dukkan waɗanda lamarin ya shafa cikin gaggawa.

Ya ce: “Na tabbatar da faruwar lamarin ne daga bakin babban jami’in ofishin ’yan sanda DPO na unguwar lokacin da na zanta da shi ta wayar tarho.

“Ina so in tabbatar muku cewa, rundunar ’yan sandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro suna aiki tuƙuru don ganin an sako dukkan waɗanda aka yi garkuwa cikin gaggawa.”

Shima Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin Sa’idu Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.