‘’Yan bindiga sun sa mana harajin N200m’
Ƙauyukan da ’yan fashin dajin suka lafta wa haraji na fadi-tashin hada kudaden kafin cikar wa’adin da aka ba su
’Yan bindiga sun sanya harajin kimanin Naira 200 ga al’ummomin wasu kauyuka a Karamar Hukumar Zurmi da ke Jihar Zamfara.
Aminiya ta gano kauyukan da ’yan ta’addan suka kaba wa harajin suna kusa ne da garin akaura Namoda zuwa Moriki da ke karamar hukumar.
Mazuana yankunan sun bayyana cewa suna cikin tashin hankali kan yadda za su hada kudin su biya harajin kafin cikar wa’adin da ’yan bindigar suka sa musu.
Ƙauyukan da kuma harajin da ’yan fashin dajin suka lafta musu su ne:
- ’Yancin kananan hukumomi: ‘Gwamnoni na shirin daukar fansa’
- NAJERIYA A YAU: Yadda Matasa Za Su Gina Rayuwarsu Da Ta Al’umma
- ’Yan Dolen Kaura – Miliyan 15
- Gidan Zagi – Milyan N15
- Kanwa – Miliyan N20
- Kaiwa Lamba – Miliyan N26
- Gidan Dan Zara Miliyan N22
- Jinkirawa – Miliyan N16
- Dumfawa – Miliyan N16
- ’Yan Dolen Kaura – Miliyan 15
- Gidan Zagi – Milyan N15
- Ruguje – Miliyan N7
- Gidan Duwa – Miliyan N4.
- Babani – Miliyan N3
Aminiya ta gano cewa wasu ds cikin al’ummomin su biya nasu harajin a yayin ragowar suke fadi-tashin hada nasu.
Majiyar ta ce wannan tashin hankalin ya sa mazauna yankunan fara yin kananan ayyuka domin samu su biya bukatar ’yan fashin dajin.
Wani mazaunin garin Zurmi, Malam Yunusa Musa, ya bayyana cewa daga wannan makon ne harajin ya fara aiki a kan yankunan da ’yan ta’addan suka sanya.
“Abin takaici shi ne, al’ummar Turawa sun biya Naira miliyan 15, amma duk da haka ’yan bindigar sun ki sako mutanen kauyen da ke hannunsu.
“Wasu ƙauyukan da dama da kan sa wa haraji daga Naira miliyan uku zuwa miliyan 26 sun riga sun biya.”
Shi ma wani dan garin na Zurmi, Malam Haruna Ilu, mazauna wasu kauyukan sun dara zuwa birnin sun yin aikatau domin samun kudin da za a biya.
Ya ce lamarin ya yi tsananin da al’ummar yankin suke cikin tashin hankali.
Don haka ya roki gwamnati ta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya shafa.
A cewar, baya-bayan nan sojoji sun fatattaki wasu ’yan bindiga da suka kai wa wasu kauyukan da ke makwabtaka da suhari.
Din haka ya jaddada kira da a ba da muhimmanci ga samar wa yankin da tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da ’yan bindigar suke tatsar su.