‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 9 a Jami’ar Kogi
‘Yan bindigar sun kai farmaki a jami’ar ne da dare yayin da ɗaliban ke karatun jarabawa.
’Yan bindiga sun kai hari Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTEC), Osara, Okene a Jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da wasu ɗalibai tara.
Wani shaidar gani da ido ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki a jami’ar ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis yayin da ɗaliban ke karatun jarabawar da za su yi.
- Sojoji Sun Mika ’Yar Chibok Da Aka Ceto Da Yara 3 Ga Gwamnatin Borno
- An kama fasto kan lalata da ’yan mata 3 a cocinsa
Majiyar ta ce ‘yan bindigan sun shigo jami’ar ne ta cikin daji ne, inda suka afka ɗakunan karatu uku, suka fara harbi a iska.
“Sun kama ɗaliban a cikin zauren, suka fara ɗaukar su.
“Wannan lamari ya jefa makarantar cikin ruɗani, yayin da ɗaliban da suka firgita suka yi ta tururuwa suna ta gudun tsira zuwa ɓangarori daban-daban.
Bayanai sun ce galibi ɗaliban makarantar sun hallara a ɗakunan karatu domin karatu gabanin jarrabawarsu ta zangon karatu na farko da za a fara a ranar Litinin 13 ga Mayu, 2024.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ana tsakar haka ne ‘yan bindigar suka mamaye harabar jami’ar da misalin ƙarfe 9:00 na dare inda suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Lokoja.
Mista Fanwo ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakan da suka dace don ganin an dawo da ɗaliban da aka sace cikin aminci.
Ya ce, Gwamna Usman Ododo ya shimfiɗa matakai domin bin diddigin masu garkuwa da mutanen tare da tabbatar da an kuɓutar da ɗaliban da aka sace.
Haka kuma, Gwamna Ododo ya buƙaci a gaggauta damke waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati mai ci ba za ta taba miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba, yana mai jaddada cewa rahoton da gwamnati ta fitar ya nuna cewa masu garkuwa da mutane ba su da wani sukuni a jihar