’Yan bindiga sun sace basarake a Filato

Wasu mahara sun yi awon gaba da hakimin al’ummar Chip da ke Jihar Filato, Sunday Dajep, da karfin bindiga.

’Yan bindiga sun sace basarake a Filato

Wasu mahara sun yi awon gaba da hakimin al’ummar Chip da ke Jihar Filato, Sunday Dajep, da karfin bindiga.

Da misalin karfe 11 na dare ranar Laraba ne ’yan bindigar suka kutsa fadar basaraken da ke jagorantar kabilar Mhiship a Karamar Hukumar Pankshin ta Jihar Filato, suka yi awon gaba da shi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar ta samu rahoton garkuwa da basaraken kuma ta dauki mataki a kai.

A cewarsa, “Jami’an rundunarmu na bin sawun ’yan bindigar; tun lokacin da muka samu kiran neman dauki muka kaddamar da aikin kamo maharan.